
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, duk wanda ke ikirarin bai aikata komai ba bayan hawa mulki to Makahone kuma kurma ne.
Shugaban ya bayyana hakane ta bakin me magana da yawunsa, Daniel Bwala.
Ya bayyana hakanne a hirar da aka yi dashi a TVC News inda yace shugaba Tinubu ya kara yawan kudaden da Najeriya ke ajiye dasu a bankin Amurka inda kuma ya biya tarin bashin da tsohuwar gwamnatin da ya gada ta bar masa.
Ya kara da cewa kuma Shugaba Tinubu ya kara yawan kudaden da yake aikawa jihohi, yace kamin zuwan Tinubu jihohi 27 sun Talauce basa iya biyan Albashi.
Yace amma a yau babu jihar da ta Talauce ko ta kasa biyan Albashi.
Yace ba biyan Albashi ba kadai yanzu Jihohi na gudanar da ayyukan ci gaba inda yace kwanannan suka je jihar Katsina, kuma Gwamnan jihar ya tabbatar da wannan magana ta cewa a baya akwai gwamnonin da basa iya biyan Albashi.
Ya kuma ce akwai bashin karatu wanda a yanzu ‘ya’yan Talakawa na iya zuwa su nema dan su yi karatu.