
Hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC ta kama Mamud Nasidi da Yahaya Nasidi, bisa kin bayyana makudan kudaden da suke dauke dasu da suka kai dala $6,180 da da fan £53,415 a filin jirgin sama na Legas.
Jami’an kula da filin jirgin saman, (FAAN) ne suka kama masu laifin inda suka damkasu hannun EFCC.
Tuni EFCC ta sanar da cewa ta fea bincike kan wadanda ake zargin.
Wadanda ake zargin sun zo ne daga Dubai inda suke shirin wucewa zuwa Abuja.
An kuma kwace wayoyi guda 3 daga hannunsu.