EFCC ta tsare mutane biyu bisa samun su da kuɗaɗen kasashen waje a Kano.

Hukumar EFFC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta ce ta fara bincike kan wasu dubun dubatar kuɗaɗen ƙasar waje da aka kama a filin jirgin sama na Kano.
BBC ta rawaito cewa, EFCC ta ce an ga dala 86,500,305 da kuma riyal 305,150 ne cikin wata jaka lokacin da aka ga wani ma’aikacin filin jirgin mai suna Sale Bala ya yi yunƙurin ɗaukar ta ranar Lahadi.
“Bayan bincike, jami’an kwastam sun gano kuɗaɗen ne da aka ɓoye cikin zannunwan gado,” in ji EFCC cikin wata sanarwa.
“An kama Sale Bala da wani Abdullahi Tahir da ake zargin shi ne aka tsara zai karɓi jakar bayan kammala tantance ta.”
Ta ƙara da cewa kuɗin da kuma waɗanda ake zargi na tsare a hannunta, kuma za ta kai su kotu da zarar an kammala bincike.