
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa a yanzu babu sauran rashin jituwa tsakanisa da dakataccen gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara.
Ya bayyana hakane bayan ganawar da suka yi da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da daren ranar Alhamis.
Wike yace komai ya wuce.
Shima Fubara ya bayyana cewa zaman lafiya ya dawo jihar Rivers inda ya bayyana jin dadinsa da ganin wannan rana da suka yi sulhu shi da Wike.