
Fadar shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu dake babban birnin tarayya Abuja ta ware Naira Biliyan 10 a cikin kasafin kudinta na shekarar 2025 dan hada sola.
Hakan na zuwane yayin da kudin wutar Lantarki yake tashi sannan wutar ba samuwa take ba yanda ake bukata.
Rahoton ya nuna za’a saka Solar a fadar shugaban kasar ta yanda fadar zata daina dogaro da wutar Lantarkin Najeriya ta koma amfani da hasken rana.
‘Yan Najeriya da yawa da suka hada da kamfanoni tuni suka daina amfani da wutar Lantarkin inda suka koma amfani da hasken rana wajan samawa kansu wutar.