Friday, March 14
Shadow

Farashin Giya, dana taba sun kara tsada fiye komai a Najeriya>>NBS

Hukumar Kididdiga ta kasa, NBS ta bayyana cewa, farashin lemun kwalba, dana giya, dana taba dana sauran kwayoyi ne yafi kowane tashi a cikin kayan da ake amfani dasu a Najeriya.

Farashin wadannan kayayyaki kamar yanda NBS ta bayyana ya tashi da kaso 14.80 a cikin watan Janairu da ya gabata.

NBS tace kayan da suka fi tsada na biyu shine farashin kudin haya da na cin abinci a gidajen cin abinci a fadin kasarnan wanda ya tashi da kaso 14.14.

Abinda ke biye musu shine farashin kayan sawa, da tafiye-Tafiye, da takalma, wanda suma suka yi tashi sama.

Karanta Wannan  A.A Rano, AYM Shafa da Matrix Petroleum Services Limited sun kai Dangote kotu inda suka ce su ba za su sayi Man fetur daga matatarshi ba dan haka ya kyalesu su siyo daga kasashen waje

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *