
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, Farashin kayan abinci ya fadi kasa sosai biyo bayan matakan da ta dauka.
Ministan Noma, Senator Abubakar Kyari ne ya bayyana hakan a hirar da aka yi dashi a Arise TV.
Yace sun shigo da shinkafa ne dan karya farashinta ba dan saka Manoma asara ba, yace kuma shigo da shinkafar daga kasashen waje na wucin gadi ne.
Yace Najeriya na da gibin kaso 15 cikin 100 na shinkafar da ake bukata, kuma itace suka shigo da ita dan cike wannan gibi.