
Tsohon sakataren Gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya bayyana cewa, farin jinin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne yasa ya ci zabe ba wai taimakon Tinubu ba.
Boss Mustapha ya bayyana hakane a wajan kaddamar da littafin da Tsohon me magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya wallafa.
Boss Mustapha yace Duk da cewa CPC ta Buhari jiha daya gareta a wancan lokacin, Amma su suka kawo kuri’u mafiya yawa da suka baiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari nasara.