Wednesday, January 15
Shadow

‘Fiye da rabin albashina zai ƙare ne a kuɗin mota’

Masu ababen hawa sun ƙara kuɗin sufuri a Najeriya bayan ƙara kudin litar man fetur.

A ranar Talata ne Kamfanin Man fetur na Najeriya (NNPCL) ya yi ƙarin farashin man fetur, daga naira 617 zuwa 855, dangane da inda mutum ke zaune a ƙasar.

Sai dai duk da ƙarin farashin litar man fetur ɗin har yanzu ana ci gaba da fuskantar ƙarancinsa a yankunan ƙasar.

A Legas, birnin kasuwanci na ƙasar, ana samun dogayen layukan masu shiga mota kasancewar motocin safa ƙalilan ne ke lodi.

Paul Eniola Adewusi ta bayyana wa BBC cewa “yanzu na kashe naira 3,500 daga unguwar Victoria Island zuwa Mowe”.

Idenyi kuwa cewa ya yi “na biya kudin mota naira 2,000 daga Lakowe zuwa Victoria Island”.

Yayin da Mmrimara Ugo ta ce “asalin kudin mota da nake biya 800 ne, amma a jiya sai da na biya naira 1,900, na ma rasa halin da nake ciki.”

Haka nan abin yake a saurarn jihohi na ƙasar.

Buƙatar man fetur ɗin da kuma ƙarin kudi da aka yi su ne abubuwan da suka haifar da tashin farashin sufurin.

‘Kashi 60% na albashina zai tafi kan sufuri ne’

Blessing Adem, ma’aikaciyar tarbar baƙi ce a ofishin wata ƙungiya mai zaman kanta da ke Abuja, tana zama ne a unguwar Ado, da ke cikin jihar Nasarawa, yankin na da nisan tafiyar minti 35 zuwa tsakiyar Abuja, inda ofishinta yake.

Karanta Wannan  Gwamnoni sun kai ziyarar jaje zuwa Maiduguri

Bayan wannan ƙarin farashin man fetur, za ta riƙa kashe naira 52,000 kan kuɗin mota a kowane wata domin zuwa aiki da komawa gida, wannan ya zarta kashi 60 cikin ɗari na albashin da take karɓa a kowane wata.

“Da safiyar nan, na biya naira 300 a matsayin kuɗin acaɓa daga ƙofar gidana zuwa bakin titi, a baya naira 100 ne ko 150.

Daga inda nake hawa mota zuwa ginin ofishin NNPC nai 1,000 ne. Zan kashe 1,300 ke nan zuwa aiki, kuma haka zan sake kashe 1,300 wajen komawa gida. Kuɗin mota ke nan kawai zan kashe 2,600 a kowace rana, ban da na abinci ke nan. Ka gani, to nawa ne albashina?” In ji ta.

BBC ta gano cewa kuɗin mota daga unguwar Nyanya, wadda ke maƙwaftaka da birnin Abuja, zuwa tsakiyar birnin na Abuja – inda akasarin ofisoshin gwamnati suke – ya kama ne daga naira 800 zuwa 1,000.

A baya kudin motar na kamawa ne daga naira 400 zuwa 500.

Karanta Wannan  An yi Allah wadai da wadannan matan saboda yanda suke kiran sauran mata da su je su bayar da kansu maza su basu kudi

Haka nan ma abin ya fara shafar kudin sufuri tsakanin garuruwa da jihohi.

Daga Abuja zuwa Gusau an samu ƙarin naira 1,000 a ranar Laraba inda ake biyan naira 15,000 a maimakon 14,000 da ake biya a baya, haka nan ma an samu ƙarin naira 2,000 a kuɗin mota tsakanin Abuja zuwa Sokoto, inda ake biyan naira 20,000 a maimakon 18,000 da aka saba biya a baya.

Farashin tafiya daga Abuja zuwa Legas a mota yanzu na kamawa ne daga naira 30,000 zuwa 43,000, dangane da kamfanin sufurin.

A baya ana biyan naira 25,000 ne zuwa 40,000 a matsayin kuɗin mota daga Abujar zuwa Legas.

Su ma masu motocin hawa na kansu ba a bar su a baya ba, domin lamarin ya shafe su. A yanzu ana cika tankin mota ƙirar Toyota Corolla, lita 55 ne a kan kudin naira 50,000 a kan farashin litar man fetur ɗaya, naira 897 ke nan, kamar yadda ake sayarwa a wasu gidajen mai na NNPC.

Abubuwa sun sauya cikin ƙiftawar ido

Zarumi Ciroma, wanda ya tattauna da BBC lokacin da yake kan layin shan man fetur a wani gidan mai na NNPC ya ce ba ya da wata mafita illa ya jira a kan layi, saboda yana da wata tafiya mai muhimmanci da zai yi daga Abuja zuwa Gusau, jihar Zamfara.

Karanta Wannan  Hoto: Davido ya nuna yanda yayi zabe a kasar Amurka, Saidai 'yan kasar Africa ta kudu sunce karya yake a bola ya dauki kuri'ar yayi hoto da ita dan ace shi dan America ne

A lokacin da ake cika wa Ciroma tankin motarsa ƙirar Honda Accord, babu abin da yake yi sai girgiza kai, ganin cewa ya ci kudi har naira 51,000.

A cikin takaici, ya tuno lokacin da ya ce yana cika tankin motarsa kan kuɗi ƙasa da naira 12,000 kafin shugaban ƙasar Bola Tinubu ya cire tallafin man fetur a watan Mayun 2023.

A wancan lokacin farashin litar man fetur na kamawa ne tsakanin naira 187 zuwa 195.

Yanzu shekara ɗaya ke nan bayan da gwamnati ta cire tallafin man fetur, amma ji ake yi kamar wasu shekaru ne masu yawa ganin yadda abubuwa suka yi gagarumin sauyawa tsakanin wannan ɗan tsukun lokaci.

Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC) a ranar Talata ta buƙaci a janye ƙarin farashin man fetur ɗin nan take, saboda a cewarta “lamarin zai ƙara tsunduma ƴan Najeriya cikin tsanani.”

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, shugabanta, Joe Ajaero ya zargi shugaba Tinubu da karya alƙawarin da suka yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *