Sunday, December 14
Shadow

Fusatattun Matasa sun Bankawa jami’in NDLEA wuta ya kone kurmus a Kaduna

Fusatattun matasa a garin Gadan Gayan dake karamar hukumar Igabi jihar Kaduna sun bankawa wani jami’in hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA me suna Aliyu Imran wuta ya kone kurmus.

Lamarin ya farune bayan da Aliyu me mukamin Assistant Superintendent of Narcotic 1 tare da abokan aikinsa suka bi wani da ake zargi da safarar kwaya inda ya tsere a mota.

Saidai garin gujewa ma’aikatan motar wanda ake zargin ta yi hadari inda hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 3.

Daga nan ne dai Aliyu yayi kokarin kwantar da tarzomar inda anan fusatattun matasa suka dakeshi tare da caka masa wuka.

Karanta Wannan  Ina Son In Sanar Al'ummar Jihar Katsina Da Ku Cewar "Shugaban Kasa Bola Tinubu Zai Zo Jihar Katsina Kuma Ya Kwana, Wanda Bai Taɓa Yi Ba A Cikin Jihohin Najeriya, Bayan Mahaifarsa Jihar Legas, Domin Taya Mu Murna Da Kuma Ƙaddamar Da Ayyuka. Ina Kira Ga Al'ummar Jihar Katsina Su Fito Tarbar Shugaban Kasa".

Anan ‘yansanda suka daukeshi suka kaishi Asibiti, saidai daga baya matasan sun bishi har asibitin inda suka janyoshi suka banka mai wuta ya kone kurmus.

Lamarin ya farune a ranar Juma’ar data gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *