
Kungiyar kwadago NLC ta koka da cewa albashin dubu 70 da ake biyan ma’aikata a biyan kudin wutar Lantarki da sayen katin waya yake karewa.
Shugaban kungiyar ta NLC, Joe Ajaero ne ya bayyana hakan ga manema labarai.
Ya bayyana cewa hakanan masu gidajen haya da ababen hawa na haya duk sun kara kudi.
Yace zasu hada kai da tawakararsu kungiyar TUC dan kwatarwa da talakawa ‘yanci.