
Mawakin kasar Ingila, Ed Sheeran ya bayyana cewa, sai da ya makance gaba daya ya daina gani bayan da ya biyewa mawakin gambara na kasar Amurka, Snoop Dog suka sha wiwi tare.
Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta.
Ed Sheeran dai ya taba bayyana cewa ya sha wiwi tare da mawakin Najeriya, Burna Boy wanda ya bayyana a matsayin daya daga cikin wanda suka fi shan wiwi da ya taba gani.