Maganar kwace gidaje 753 daga hannun tsohon gwamnan babban banking Najeriya, CBN, Godwin Emefiele ta jawo cece-kuce tsakanin hukumar EFCC da mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore.
EFCC a yayin da ta wallafa maganar kwace gidajen tace an kwacesune kawai daga hannun wani babban jami’in Gwamnati ba tare da fadar sunanshi ba.
Dalilin hakane Sowore ya zargi EFCC da yin rufa-rufa akan lamarin inda yace daga hannun Emefiele ne aka kwace gidajen.
Saidai EFCC ta musanta hakan, a martaninsa, Sowore ya wallafa takardun kotun Wanda suka nuna yanda aka zartar da hukuncin kwace gidajen da sunayen mutanen sake da hannu a lamarin.