
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, gajarta ce tawa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai yawa shiyasa yake ta soki burutsu.
Ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Bayo Onanuga.
El-Rufai a wata hira da aka yi dashi yace a wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da suka gudanar sun gano cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba zai ci zaben shekarar 2027 ba.
Saidai Onanuga yace babbar matsalar El-Rufai shine shi a ko da yaushe yana son ya nuna yafi sauran mutane.
Yace El-Rufai bashi da biyayya inda yawa mutane da yawa a baya ciki hadda wansa wanda tsohon soja ne.
Yace kuma makaryaci ne sosai wanda ke yin abubuwa yawanci dan kawai amfanin kansa.