
Jigo a jam’iyyar PDP tsohon gwamnan jihar Jigawa Alh.Sule Lamiɗo, ya yi hasashen cewa za a samu ɓarkewar rikici mai girma a jam’iyyar APC, inda ya ce nan da ɗa wani lokaci kaɗan jiga-jigai a Jam’iyyar APC, ciki har da shugaban jam’iyya na ƙasa, Dr.Abdullahi Umar Ganduje za su iya komowa cikin jam’iyyar PDP.
Lamiɗo ya bayyana haka ne ya yin gangamin taron da aka gudanar a filin taro na Aminu kano Triangle a babban birinin jiha Dutse a lokacin zaɓan shuwagabannin jam’iyyar a matakin jiha.
Ya ce “Na tabbatar da cewa waɗanda suka bar jam’iyyar PDP za su dawo, domin APC a cike take da rigima kuma nan ba da daɗewa ba gayyar za ta watse” ~Sule Lamiɗo
Ya ƙara da cewa “Ku rubuta ku a jiy, nan da watanni shida da yawa daga cikin waɗanda suka koma j’iyyar APC za su dawo PDP, kuma idan suka yi hakan PDP za ta sake yin ƙarfi mu karɓe mulki a kakar zaɓe ta 2027.”