A baya-bayan nan an yi ta raɗe-raɗin cewa jagororin hamayyar Najeriya da suka haɗa da Atiku Aubakar na PDP, da Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP da kuma Peter Obi na LP na shirin dunkulewa wuri guda don tunkarar APC a zaɓen da ke tafe.
Sai dai tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya fito fili ya nesanta kansa da rahotannin da ke cewa sun amince da yin mulki na wani wa’adi kowannesu, wato karɓa karɓa a tsakaninsu.
Tsohon gwamnan na Kano ya kuma nuna rashin jin daɗinsa da abin da ya kira shisshigin da wasu dattawan arewacin ƙasar ke yi wajen fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa, abin da ya ce na janyo raba kan al’umma.
A hirarsa da Imam Saleh, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya taɓo batutuwa da dama ciki har da siyasar jihar Kano, inda wasu ke ta kira ga gwamna Abba Kabir Yusuf ya tsaya da kafarsa, wato ya raba gari da shi kenan, amma ya fara ne da bayyana ra’ayinsa kan dokar harajin da ta janyo cece-kuce a ƙasar.