
Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin ya jinjinawa baban Malamin Addinin Islama, Sheikh Ibrahim Maqari bisa fatawar da ya bashi cewa, yana iya ci gaba da yin Bidiyo da matarsa yana dorawa a kafar sada zumunta.
Gfresh yace haka ya kamata kowane malami ya kasance sannan yayi kira da a rika samunta addinin musulunci yana zama daidai da zamani.
Gfresh ya kuma yi kiran cewa ya kamata a a daina zagin malamai inda yace shi kome za’a fada akansa a fada amma a daina zagin malamai.