‘
Yan kasuwar man fetur sun koka da sarar da suka tafka bayan da kamfanin mai na kasa NNPCL ya rage farashin man da yake sayarwa.

A Legas, NNPCL na sayar da litar man fetur din aka farashin Naira 880 kan kowace lita yayin da a Abuja kuma NNPCL din na sayar da man fetur din akan farashin 935 akan kowace lita.
Hakan na zuwane sati daya bayan da Dangote ya rage farashin man fetur din nasa.
A Legas, Farashin man fetur din na NNPCL yafi na Dangote Arha da Naira 10.
Saidai kamfanin na NNPCL ya baiwa ‘yan kasuwar damar su sayar da tsohon man da suke dashi kamin fara amfani da sabon farashin.