
jam’iyyar APC ta caccaki tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai inda ta bayyanashi a matsayin wanda ke ci ke da girman kai da haushi saboda bai samu mukamin minista ba.
Sakataren jam’iyyar, Felix Morka ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.
Yace El-Rufai ya kamata idan zai soki gwamnatin Tinubu yayi suka ta adalci.
Felix yayi watsi da ikirarin El-Rufai na cewa jam’iyyar APC ta kauce daga kan turbar da aka kafata inda yace gwamnatin Tinubu ta samu ci gaba sosai da suka hada da cire tallafin man fetur da daidaita canjin kudi da sauransu.