Saturday, March 15
Shadow

Gobara ta ƙone shaguna fiye da 100 a kasuwar Zamfara

Wata gobara a babbar kasuwar Gusau da ke jihar Zamfara ta laƙume aƙalla shaguna 103 a ɓangaren kayayyakin abinci masu saurin lalacewa da ke kasuwar.

Duk da dai ba a gano dalilin faruwar gobarar ba, ɗaya daga cikin masu kashe gobarar ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa gobarar na da alaƙa da wutar lantarki inda ya ce gobarar ta kama ne jim kaɗan bayan kawo wuta a kasuwar.

A cewarsu, gobarar ta soma ne da karfe 10:30 na daren Lahadi kuma ta shafe sa’oi ta na ci kafin ma’aikatan hukumar kashe gobar na jihar da na tarayya suka yi nasarar kashe ta da karfe biyun dare.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo yanda aka wulakanta wani barawon Kunin Aya inda aka sashi yace shi barawo ne ya saci kunun aya

Shugaban kungiyar masu sayar da kayan abinci da ke saurin lalacewa, Alhaji Inusa Saminu ya shaida wa jaridar ta Daily Trust cewa lamarin ya munana, kuma zuwa yanzu ba za su iya kirga asarar su ba sai dai ya ce sun kai miliyoyi.

Ya ɗora alhakin ta’azarrar gobarar kan rashin isowar ma’aikatan kashe gobarar kan lokaci inda ya ce sun kira masu kashe gobarar na kusa da sai su ka ce musu motar ta lalace na tsawon watanni, wasu kuma su ka yi korafin motar ta su babu batir.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *