Wednesday, May 7
Shadow

Gwamna Bago ya janye matakin da ya ɗauka akan samari masu tara gashin dada a Neja

Gwamna Bago ya janye matakin da ya ɗauka akan samari masu tara gashin dada a Neja.

Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, ya janye umarninsa na baya da ya bayar ga jami’an tsaro da su kama masu gashin dada da maza masu Kitso a Minna, babban birnin jihar.

Bago, yayin da yake magana a wani taron tsaro tare da masu ruwa da tsaki a gidan gwamnati ranar Talata, ya umarci jami’an tsaro da su yanke gashin dada na mutanen da aka kama tare da cin tarar kudi.

Ya ce: “Duk wanda kuka gani da Gashin Dada, ku kama shi, ku yanke masa gashi, sannan ku ci shi tara.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Tinubu dan Kanone>>Inji Ganduje

“Babu wanda zai rika yawo da irin wannan gashi a cikin Minna. Na riga na ba da umarni ga jami’an tsaro,” in ji gwamnan.

Sai dai a ranar Laraba, gwamnan ya janye wannan umarni bayan ya fuskanci suka daga ‘yan Najeriya da dama.

Yayin da yake gayyatar masu zuba jari zuwa Jihar Neja, gwamnan ya bukaci duk wanda ke da niyyar kafa kasuwanci a jihar da kada ya ji komai, ya zo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *