
Gwamnan jihar Kano dake arewacin Najeriya Abba Kabir Yusuf, ya ayyana Litinin, 2 ga Yuni, a matsayin ranar hutu domin bawa al’umma su yi addu’a da jimamin ƴan wasan jihar 22 da suka rasu a hatsarin Mota ranar Asabar.
Gwamnan ya kuma bayyan alhini tare da miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan mamatan.
Wannan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Asabar 31 ga Mayu, 2025.
Haka kuma gwamna Abba ya bukaci limamai da ɗaukacin musulmi dake gida da na ƙasa mai tsarki da suka je aikin hajji su yi addu’ar neman rahama ga mamatan da kuma juriya ga iyalansu.