Gwamnan Kano Abba zai kori kwamashinonin da ba su da himma.
Gwamnan jihar Kano a arewacin Najeriya ya bayyana aniyarsa ta sauke duk wani kwamashinansa da “aka gano ba shi da himm” a aikinsa nan gaba kaɗan.
Wata sanarwa da mai magana da yawunsa Sanusi Bature ya fitar ta ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamatin da ke duba ƙwazon kwamashinonin.
“Nan gaba kaɗan al’umma za su ji matakin da gwamnatin za ta ɗauka,” in ji sanarwar.
Ya ƙara da cewa “gwamnan ya ce rahoton ma ba zai yi wani amfani ba yanzu saboda tsawon shekara ɗaya da rabi da ya yi yana aiki ntare da su ya ba shi damar gane himmarsu ciki da baya, saboda haka da kansa zai yanke hukuncin”.
Yanzu haka dai jam’iyyar NNPP mai mulki a Kanon na fama da rikici, musamma a ɓangaren ƙungiyar Kwankwasiyya da tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso ke jagoranta, inda wasu ‘jiga-jigai suka ce sun fita daga cikinta.