Friday, December 5
Shadow

Gwamnati ta ƙara yin gargaɗi kan yiwuwar ambaliya a wasu jihohin Najeriya

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya NiMet ta ce akwai yiwuwar wasu jihohin Najeriya su fuskanci ambaliya a daminar bana.

Wata sanarwa da NiMet ta fitar a shafinta na X, ta ce jihar Akwa Ibom ce tafi barazanar fuskantar ambaliyar a yanzu.

Sauran jihohin sun haɗa da Sokoto, Zamfara, Plateau, Yobe, Bauchi da kuma Bayelsa.

Sai Nasarawa da Benue da Ogun da Ekiti da Delta da kuma Ribas.

Don haka ne hukumar ta gargaɗi jama’a, musamman waɗanda ke jihohin da lamarin zai iya shafa, da su riƙa yashe magudanan ruwa domin buɗe wa ruwa hanyar wucewa.

Ta shawarce su da su riƙa yin nesa da wuraren da ke da haɗarin ambaliya, inda ta ce in ta kama su tashi daga waɗannan wurare.

Karanta Wannan  BA RABO DA GWANI BA: Yau Shekara 15 Da Rasuwar Tsohon Shugaban Ƙasa Ummaru Musa Yar'adua

A kowace shekara dai, ambaliya na yin sanadiyyar rayukan mutane da dama da kuma lalata gidaje a Najeriya.

Ko a kwanaki nan ambaliya ta afka wa garin Mokwa da ke jihar Neja, abin da ya janyo mutuwar aƙalla mutum 230.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *