
Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar 3 ga watan Afrilu da kuma Litinin 6 ga wata a matsayin ranekun bukukuwan Easter.
Ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan a madadin Gwamnatin tarayya inda yace suna taya Kiristoci murnar wannan rana.
Ya kuma yi kiran cewa, Kiristocin su yi koyi da halaye na gari na Jesus.