
Gwamnatin jihar Borno ta amince da kudurin haramta sare itatuwa ba bisa ka’ida ba a faɗin jihar.
Gwamna Babagana Umara Zulum ne ya sanar da haka ranar Juma’a, inda ya ce an ɗauki matakin ne domin kare muhalli da inganta lafiyar al’umma.
Haka kuma, gwamnan ya amince da kudurin tsaftace muhalli wanda za a riƙa yin shara a a kowace Asabar ɗin farkon wata a faɗin jihar.
“A don haka, duk wani mutum da aka samu yana sare itatuwa ba bisa ka’ida ba, za a ci tararsa naira 250,000 ko kuma ɗaurin shekara uku a gidan yari. Idan ya sake aikata laifin, hukuncinsa shi ne ɗaurin shekara biyar ko tarar naira 500,000 ko kuma a zartas masa da duka hukuncin,” in ji gwamna Zulum.
Gwamnan ya ce waɗanda aka samu ba sa tsaftace muhallinsu za a ci su tarar da ta kai naira 100,000 saboda saɓa wa umarnin da aka kafa na tsaftace muhalli.
Ya ƙara da cewa an ɗauki matakin ne domin kula da lafiyar al’umma da kuma rage yaɗuwar cutuka tsakanin al’ummomi.