Saturday, March 15
Shadow

Gwamnatin jihar Sokoto ta fara biyan malaman firamare mafi ƙanƙantar albashi

Makonni uku bayan wani rahoton da BBC ta yi game da ƙorafin da malaman makarantun firamaren jihar Sokoto suka yi na rashin biyansu sabon albashi mafi ƙanƙanta na naira 70,000, gwamnatin jihar ta biya su, har ma da yi musu ƙari.

Malaman makarantun firamaren sun shaida wa BBC irin farin cikin da suka ji game da alƙawarin da gwamnan jihar, Ahmad Aliyu ya cika, na biyansu sabon albashin kamar kowa tare da sauran ma’aikatan gwamnatin jihar da suka hada da na kananan hukumomi 23.

Mai magana da yawun gwamnan jihar, Abubakar Bawa, ya shaida wa BBC cewa gwamnatin ta saurari ƙorafin da ma’aikatan suka yi ne, shi ya sa ta cika alƙawarin da ta ɗaukar musu tun da farko.

Karanta Wannan  Na karbi mulki Najeriya na cikin wahala da matsin tattalin arziki shiyasa na dage dan kawo gyara>>Shugaba Tinubu

A watan Yulin shekarar 2024 ne, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da ƙara albashi mafi ƙanƙanta ga ma’aikatan ƙasar daga naira 30,000 zuwa 70,000.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *