Monday, May 5
Shadow

Gwamnatin Kaduna ta ƙwace gidajen da El-Rufa’i ya sayar

Gwamnan jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, Uba Sani ya bayar da umarnin ƙwace gidaje da filayen da tsohuwar gwamnatin da ta shuɗe ta Malam Nasiru El-Rufa’i ta sayar a jihar.

Gidajen da filayen da aka ƙwacen sun haɗa da waɗanda tsohon gwamnan ya sayar a kwalejin Queen Amina da ke Kaduna da kwalejin Alhuda-huda da kwalejin Government Commercial da ke Zaria.

Umarnin na ƙunshe ne a wata sanarwar da aka fitar, a ranar Talata da daddare, mai ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar, Dr AbdulKadir Mu’azu Meyere.

Sanarwar ta bayyana cewa an ƙwace gidajen da filayen ne saboda amfanin al’umma.

Sai dai an jima ana takun saƙa tsakanin gwamna Uba Sani mai ci yanzu, da kuma wanda ya gada, Malam Nasir El-Rufa’i.

Karanta Wannan  Muna matukar godiya da hakuri da kuke yi da wahalar da tsare-tsaren gwamnatin mu suka jefa ku ciki amma yanzu lamura sun fara Gyaruwa>>Gwamnatin Tarayya ga 'yan Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *