
iGwamnatin jihar Kano ta rufe wajan shan shisha me suna Arfat Shisha Lounge
Hukumar kula da yawon shakatawa ta jihar hadi da hukumar yaki da shan miyagun kwayoyi, NDLEA ne suka rufe wajan shan shishar.
Shugaban hukumar shakatawar Alhaji Tukur Bala Sagagi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa inda yace wannan kokari ne na kawar da ayyukan ta’ammuli da miyagun kwayoyi a jihar.
Yace a jihar ta Kano, Akwai dokar Haramta shan Shisha kuma zasu ci gaba da karfafa wannan doka.