Friday, December 5
Shadow

Gwamnatin Katsina ta nemi a soke jarabawar WAEC ta turanci

Gwamnatin Katsina ta nemi a soke jarabawar WAEC ta turanci.

Gwamnatin Jihar Katsina a ranar Asabar ta nemi a soke jarabawar harshen Turanci da Hukumar Jarabawa ta Yammacin Afirka (WAEC) ta gudanar kwanan nan.

Wannan kiran ya biyo bayan wani lamari da ya haifar da jinkiri mai tsawo kafin fara jarabawar a fadin kasar nan a ranar Laraba.

Matsayar gwamnatin jihar ta fito ne daga bakin Kwamishinar Ilimin Firamare da Sakandare, Zainab Musa-Musawa, lokacin da ta kai ziyara ofishin WAEC da ke Katsina.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa wannan matsaya ta samo asali ne daga wata takardar korafi da Babbar Sakatariyar ma’aikatar, Hajiya Ummukhair Ahmed ta sanya wa hannu.

Karanta Wannan  Mu a yankin Inyamurai da kaso 95 cikin 100 Kiristoci ne, 'yan uwan mu Kiristoci ne ke shekye mutanen mu>>Inji Gwamnan Anambra, Charles Soludo

A baya dai, WAEC ta danganta jinkirin fara jarabawar da ƙoƙarinta na hana magudin jarabawa, musamman yaduwarsu kafin lokacin da ya dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *