Friday, December 26
Shadow

Gwamnatin Najeriya karya take, Amurka bata sanar da ita Khàrìn data kai sokoto ba>>Inji Omoyele Sowore

Mawallafin Jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore ya bayyana cewa, Gwamnatin tarayya karya take Amurka bata sanar da ita ba kamin ka harin Sokoto.

A safiyar yau ne dai aka tashi da rahoton cewa, Kasar Amurka ta kai hari Kan wanda ta zarga da yiwa Kiristoci Khisan Kyiyashi.

Sowore dai yace wannan abin kunyane ace kasa Kamar Najeriya ta koma ‘yar kallo wajan magance matsalar tsaronta sai an zo an taimaka mata.

Sowore yace Idan aka samu shugabanci na gari, Najeriya zata samu tsaro.

Karanta Wannan  Dalibar Da Ta Kammala Digiri Da Sakamako Mafi Daraja A Jami'ar Northwest Dake Kano Ta Koma Tallar Wainar Fulawa Bayan Rashin Samun Aikin Yi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *