Friday, December 5
Shadow

Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da wani shirin tabbatar da amfani da gas wurin girki ya shiga yankunan arewacin Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da wani shirin tabbatar da amfani da gas wurin girki ya shiga yankunan arewacin Najeriya.

Karamin ministan man fetur na Najeriya, Ekperikpe Ekpo ne ya ƙaddamar da shirin yau Alhamis a garin Sokoto.

Lokacin da yake jawabi a wurin ƙaddamar da shirin, gwamnan jihar Ahmed Aliyu ya ce matakin zai taimaka wajen rage dogaro kan amfani da itace a wajen girki, lamarin da ke cutar da muhalli musamman a jihohin Najeriya da ke iyaka da hamada.

Sai dai ya buƙaci masu ruwa da tsaki su yi ƙoƙarin ganin farashin gas ɗin ya yi daidai da ƙarfin talaka.

“Matuƙar ana so wannan shiri ya yi tasiri dole ne sai an samar da gas din LPG a wadace kuma cikin rahusa ga mutanen Najeriya masu matsakaicin karfi,” in ji gwamnan.

Karanta Wannan  Hotunan Yayar Gwamnan Jihar Katsina Kuma Mai Ɗakin Tsohon Shugaban Kasa, Malam Umaru Musa Yar'adua, Hajiya Hauwa Radda A Wajen Bikin Diyar Gwamnan Katsina A Ranar Asabar Da Ta Gabata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *