Gwamnatin sojin Nijar ta hana sojoji yin ritaya

A jamhuriyar Nijar, gwamnatin mulkin sojan ƙasar ta ce ta ɗauki matakin hana jami’an tsaro yin ritaya a wannan shekara ta 2025 ko da kuwa shekarunsu sun kai na ajiye aikin.
Wannan matakin na ƙunshe ne cikin wata takarda da ministan tsaro na Nijar, Janar Salifu Modu, ya aike wa hafsan hafsoshin sojin ƙasar, inda ya buƙaci a riƙe ɗaukacin sojojin da shekarunsu suka kai su yi ritaya daga aikin tsaro bisa la’akari da ɗimbin ayyuka da kuma alƙawuran da ke gaban sojojin a duka fadin ƙasar.
Hukumomin tsaron ƙasar sun ce sun ɗauki wannan mataki ne saboda buƙatar da ke da akwai ta ƙarin sojoji a fagen daga musamman yadda ƙasar ke ci gaba da fuskantar hare-hare daga kungiyoyi masu ɗauke da makamai a yankunan ƙasar da dama.
Shugaban ƙungiyar tsofaffin sojoji, Musa Tankadiya, ya shada wa BBC alfanun wannan mataki ga yaƙin da ƙasar ke yi da ta’addanci.