
Gwamnatin tarayya ta bayyana Albashi da alawus din da ake biyan Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima
Albashi da alawus din da ake biyan mataimakin shugaban kasar ya kai Naira Miliyan ₦12,126,290 a shekara.
Ainahin Albashin mataimakin shugaban kasar wanda babu Alawus shine Naira ₦3,031,572.50 a shekara wanda yana nufin Naira ₦252,631.04.
Daya daga cikin Alawus din da mataimakin shugaban kasar yake dauka shine na Naira ₦1,515,786.25 a shekara a matsayin alwus din wahalhalun da yake.
Sannan akwai Alawus din mazabarsa na Naira ₦7,578,931.25 da ake bashi shima duk shekara.