
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya ta ciwo bashi fiye da yanda ta yi niyyar ciyowa a shekarar 2025.
A kasafin kudin shekarar 2025, Gwamnati ta yi niyyar ciwo bashin Naira Tiriliyan 13.08 saidai zuwa yanzu har ta ciwo bashin Naira Tiriliyan 17.36.
Hakan na nufin Gwamnatin ta ciwo bashin Naira Tiriliyan N6.06 sama da abinda ta yi niyyar ciyowa a wannan shekarar tun ma shekarar bata kare ba.
Gwamnatin taci bashin naira Tiriliyan N15.8 daga cikin gida Najeriya sai kuma bashin Naira Tiriliyan 1.56 daga kasashen waje.
A satin daya gabata ne dai Gwamnatin ta bayyana aniyar son ciwo bashin Naira Tiriliyan N3.384 daga kasashen Turai.