Gwamnatin tarayya ta gabatar da kasafin kudin Naira Tiriliyan N47.9trn a matsayin kasafin kudin shekarar 2025.
Ministan kasafin kudi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ne ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Alhamis bayan zaman majalisar zartaswa.
Yace nan da ranar Juma’a ko Litinin ake tunanin gabatarwa da majalisar tarayya da kasafin kudin a hukumance.