
Gwamnatin tarayya tace daga yanzu ba za’a kara barin tankokin dakon man fetur su rika tuki da dare ba.
Ta bayyana hakane ta bakin shugaban hukumar kula da hadahadar Man fetur ta kasa, Farouk Ahmed, a wajan wani taro.
Yace daga yanzu Direbobin tankar zasu rika tuki ne daga 6 na safe zuwa 6 na yamma.
Yace an dauki wannan mataki ne dan magance matsalar hadurran tankar mai wadda ta jawo hasare rayuka da Dukiyoyi q baya.
An yi taronne da hadin gwiwar direbobin tanka, da hukumar kiyaye hadurra ta kasa, Road Safety da Kungiyar ma’aikatan fetur na kasa da sauransu.
Yace duk direban da aka kama yana tuki da dare zai fuskanci hukunci.