Wednesday, May 28
Shadow

Gwamnatin tarayya ta saka dokar ta baci a Onne saboda shigo da miyagun makamai Najeriya

Hukumomi a Najeriya sun saka dokar ta baci akan tashar ruwa dake onne jihar Rivers.

Hakan ya biyo bayan jiragen ruwa da akai ta kamawa suna dauke da miyagun makamai ne da ake shirin shigowa dasu Najeriya.

Lamarin yayi kamari ta yanda an baza jami’an tsaro a tashar jirgin ruwan wanda kuma duk kayan da aka kawo sai an bincikasu yanda ya kamata.

Shugaban hukumar Kwastam, Bashir Adeniyi, ne ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai inda yace hakan na barazana ga tsaron Najeriya.

Karanta Wannan  Dalla-Dalla: Sanata Natasha Akpoti ta fitar da kalaman batsa da Sanata Godswill Akpabio ya gaya mata bayan da ta je ofishinsa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *