Gwamnatin tarayya a cikin kasafin kudin shekarar 2025 ta ware Naira Biliyan 100 dan ciyar da yara ‘yan Makarantar Firamare.
Tsarin ciyarwar an fito dashi ne dan kawar da matsalar rashin samun abinci me gina jiki da yaran ke fama da ita da kuma karfafa ilimi da karfafa gwiwar manoma.
A kokarin inganta tsarin, Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, zata yi kokarin ganin an magance matsalolin shirin kama daga rashin biyan masu aikin da manoma da rashin baiwa daliban abinci me kyau.