Friday, December 26
Shadow

Gwamnatin tarayya ta warewa jama’ar jihar Bayelsa da Rivers tallafi da bashin Naira Miliyan 200, sai rokonsu ake su je su karba

Gwamnatin tarayya ta warewa jama’ar jihohin Rivers da Bayelsa bashi me hade da tallafi na Naira Miliyan 200 ta hanyar bankin manoma na tarayya watau BOI.

Kowacce jiha a cikin jihohin biyu an ware mata Naira Miliyan 100.

Saidai mutanen jihar basa zuwa karbar wannan bashi, dalili kenan da yasa bankin na BOI ya nuna damuwa hadi da kiran cewa mutanen wadannan jihohi su zo su nemi wannan bashi.

Shugaban bankin na yankin Pacqueens Irabor ne ya bayyana hakan inda yace mutum daya zai iya neman bashin Naira Miliyan 10 kuma za’a biya bashin ne nan da shekaru 3.

Yace kaso 40 cikin 100 na bashin tallafi ne, kaso 60 ne kawai mutum zai biya.

Karanta Wannan  Wata mata ta Shekye aurenta saboda rikicin kudin kwalliya da mijinta ya ki bata

Yayi kira ga ‘yan kasuwa da kananan masana’antu da su je su karbi wannan bashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *