Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya na shirin rage yawan danyen man fetur din da take sayarwa da kamfanin matatar man Dangote.
Hakan na zuwane bayan da matatun man fetur na Gwamnati, na Fatakwal dana Warri suna dawo suka ci gaba da aiki.
Rahoton jaridar Punchng ya ruwaito cewa dan samarwa wadannan matatun man fetur na gwamnati isashshen danyen man fetur din, Gwamnatin zata rage yawan danyen man fetur din da take sayarwa matatar man fetur ta Dangote.
Hakan, a cewar masana tattalin Arziki, zai sa a samu gasa sosai a kasuwar man fetur din wanda hakan zai yi sanadiyyarf faduwar farashin man fetue din.