
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa kudaden jihar Rivers da aka rike zasu sakarwa gwamnatin rikon kwarya ta jihar karkashin kulawar Vice Admiral Ibok Ibas (retd).
Gwamnatin tace matakin da shugaba Tinubu ya dauka a jihar Rivers ya daukeshi ne a daidai lokacin da ya dace dan kaucewa lalacewa al’amura a jihar.
Gwamnatin ta kuma ce, Tsohon gwamnan jihar, Nyesome Wike bashi da hannu a wajan rikicin siyasar jihar da ya kai ga saka dokar tabacin.
Babban akanta janat na kasa, Lateef Fagbemi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a fadar shugaban kasa dake Abuja ranar Laraba.
Ya bayyana cewa shin sai yaushene ake son ganin shugaba Tinubu ya dau wannan mataki? Yace sai abubuwa sun rinchabe? Yace yanzu ne daidai lokacin da ya kamata a dauki matakin.