Friday, December 26
Shadow

Gwamnonin Zamfara da Benue sun ƙalubalanci gayyatar kwamitin majalisar wakilai

Gwamnonin jihohin Zamfara da Benue, Dauda Lawal da Hyacinth Alia, sun ƙi amincewa da gayyatar da Kwamitin Karɓar Ƙorafe-ƙorafe na Majalisar Wakilai ta Tarayya ya aike musu, inda suka bayyana shakku kan halaccin gayyatar.

An gayyaci gwamnonin da majalisun dokokin jihohinsu ne domin su bayyana a gaban kwamitin bisa zargin karya ƙundin tsarin mulki da kuma gazawa wajen gudanar da mulki.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai na kwamitin, Chooks Oko, ya fitar

Sanarwar ta bayyana cewa an tsara zaman sauraron bayanansu ne a ranar 8 ga watan Maris, inda ake sa ran za su bayar da ƙarin haske kan wasu muhimman al’amura.

Karanta Wannan  Idan aka Tambayi dan tsigigi, Guntun Mugu, Wanene Ubangijinka a Kabari, zai ce Allah, idan aka tambayeshi Addininshi, zai ce Islam, amma ida aka Tambayeshi wanene shugabanka? Zai ce Buhari sai ya sha Guduma>>Inji Sheikh Zakzaky

Daga cikin matsalolin da ake son jin bayani a kansu har da dakatar da wasu ‘yan majalisar jiha da kuma taɓarɓarewar tsaro a jihohin biyu.

Hakan ya sa majalisar ke duba yiwuwar amfani da Sashe na 11(4) na Ƙundin Tsarin Mulki na 1999, domin ɗaukar ragamar ayyukan majalisun dokokin jihohin idan an ga hakan ya zama dole.

A Jihar Benue, an dakatar da ‘yan majalisa 13 bayan da suka nuna adawa da cire shugaban alƙalan jihar, Mai shari’a Maurice Ikpambese, wanda gwamnan ya jagoranta.

An dauki dakatarwar dai a matsayin ramuwar gayya ga ‘yan majalisar da ba sa goyon bayan gwamnan.

A Jihar Zamfara kuwa, lamarin shine wasu ‘yan majalisa tara da aka dakatar suka kafa wani rukunin majalisa daban, suna kuma ci gaba da iƙirarin cewa suna da cikakken ikon dokoki.

Karanta Wannan  Na yi iya lissafin da zan yi na gano cewa, Tinubu ba zai ci zaben 2027 ba, na kudu zai zo>>Inji El-Rufai

Yanzu haka, majalisar wakilai ta tarayya na ci gaba da nazarin ko lamarin ya kai matakin da ya dace a shiga tsakani ta hanyar karɓar ragamar aikin majalisun jihohin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *