
Rahotanni daga Suleja Jihar Naija na cewa, Wani bakanike me suna Yusuf Isiaka ya gamu da fushin wasu ‘yan Achaba bayan da ya buge wani daga cikinsu har ya ji rauni.
Rahoton yace Yusuf yana gida sai me gidanshi ya kirashi ya bashi mota ya je ya gyara masa.
Yana kan hanya ne sai ya buge wani dan Achaba wanda a cewar Rahoton dan Achabar ne ya fado masa, dan Achabar yaji rauni.
Anan ne ‘yan Achaba suka rufar masa da zagi da duka inda daga baya aka sasantasu, yace zai kai kara wajan ‘yansanda.
Ya hau mota ya ci gaba da tafiya kawai sai ya ji ana ihu Barawo, ‘yan Achaba da yawa a bayansa, ganin yawansu yasa bai tsaya ba ya ci gaba da tuki inda su kuma suka ci gaba da binsa suna kara yawa sai da suka kai 50.
A karshe sun cin masa suka fiddoshi daga mota suka dakeshi har ya mutu.
Rahoton yace yana da mata da tsohon ciki da diya guda daya.
Hakanan kuma akwai mahaifinsa wanda yake da shagon sayar da kaya.
Zuwa yanzu dai ‘yansanda basu kama kowa ba kan wannan lamari.