Friday, December 5
Shadow

Gyaran da nawa Najeriya yasa a yanzu ana ganin Kima da darajarmu a Idon Duniya>>Inji Shugaba Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce muhimman tsare-tsaren gwamnatinsa sun soma samar da sakamakon da ake buƙata, inda ya ce tattalin arziƙin ƙasar ya daidaita har ya soma janyo hankalin masu zuba jari daga ƙasashen duniya.

Tinubu ya faɗi hakan ne a fadar sa da ke Abuja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, a lokacin da ya karbi baƙuncin Oba Ghandi Afolabi Oladunni Olaoye, Orumogege III na Ogbomoso da tawagarsa.

A cewar shugaban, halin ko-in-kula da rashawa da fasa kauri da yaudara ne su ka hana Najeriya samun kuɗaɗen shiga da za a yi amfani da shi wajen samar da ci gaba.

”Tattalin arziƙinmu ya fuskanci barazana, wajibi ne mu ɗauki matakai ƙwarara. Amma tare da adduo’in ku da haƙuri da juriyarku, ina farin cikin shaida muku cewa a yanzu tattalin arziƙi ya dai-daita” In ji shi.

Karanta Wannan  Kalli Tsohon Shugaban Jam'iyyar APC Na Kasa Dr. Abdullahi Umar Tare Da Iyalansa A Birnin Landan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *