
A safiyar yaune muka tashi da labarin cewa hukumar Hisbah ta jihar Kano ta Haramta jin wakar Amanata ta Hamisu Breaker.
Da yawa basu san wannan waka ba kamin Hisbah ta Haramtata, sai bayan da aka Haramtata ne mutane da yawa suka fara sauraren wakar.
Bidiyon Khajida Me Numfashi data hau wakar tana bi ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda aka ganta tana rawa da rausayawa kamar wata ‘yar India.
Mutane sun bayyana mabanbanta ra’ayoyi akai sosai.