Wednesday, May 14
Shadow

Hajji 2025: Za a Fara Jigilar Alhazan Kano Ranar 13 Ga Mayu

Hajji 2025: Za a Fara Jigilar Alhazan Kano Ranar 13 Ga Mayu

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta bayyana cewa za a fara jigilar alhazan jihar zuwa ƙasa mai tsarki a ranar 13 ga Mayu, 2025.

Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da Sulaiman A. Dederi, Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar ya fitar.

Shugaban hukumar, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ne ya sanar da hakan yayin wata ziyara da ya kai cibiyoyin bita na kananan hukumomin Ungogo da Bichi, a wani bangare na shirin Hajjin shekarar 2025.

Ya bayyana cewa, bisa ga jadawalin da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta fitar, za a fara jigilar alhazan Kano ta jirgin Max Air. Alhaji Lamin ya ce tuni hukumar ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka wajaba don tabbatar da nasarar jigilar alhazan cikin tsari da kwanciyar hankali.

Karanta Wannan  Fafaroma da ya mutu yau na ta shan yabo saboda goyon bayan 'yan Luwadi da Madigo

A nasa jawabin, shugaban kwamitin koyar da aikin Hajji, Alhaji Yusif Lawan, ya ja hankalin mahajjata su rika halartar darussan koyon Aikin Hajji domin amfanar kansu da kuma sauƙaƙa musu gudanar da ibadar.

Ya kuma gargadi mahajjatan da su kiyaye bin dokokin Najeriya da na ƙasar Saudiyya, domin guje wa duk wani abu da ka iya kawo tsaiko a lokacin gudanar da aikin Hajjin.

Shugaban hukumar tare da mambobin kwamitinsa da daraktoci sun halarci wannan muhimmiya ziyara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *