
Hukumar bayar da lamuni ta Duniya, IMF ta bayyana cewa, har yanzu akwai talauci sosai a Najeriya.
Hukumar tace har yanzu Najeriya na fuskantar rashin tabbas game da tattalin arziki duk da gyare-gyaren data gudanar.
Shugaban hukumar a Najeriya, Axel Schimmelpfennig ya bayar da tabbacin cewa, Najeriya ta dauki matakai masu muhimmanci wajan tayar da komadar tattalin arziki amma matsalar itace kidaden shiga da take samu zasu samu tangarda musamman saboda faduwar farashin danyen mai a kasuwannin Duniya.
Saidai IMF tace har yanzu da yawan ‘yan Najeriya basu amfana da tsare-tsaren na gwamnatin ba inda da yawa ke fama da talauci sannan matsalar tsaro na karuwa.