
Shafin Facebook na hukumar HISBAH ta Kano har yanzu yana hannun wani bata gari da ya musu kutse kuma yace saka hotunan batsa a kansa.
Tun a watan Augusta na shekarar 2024 ne dai aka yiwa shafin kutse inda Hukumar HISBAH din ta rasa iko dashi, yanzu watanni 6 kenan.
Shugaban HISBAH, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace bangaren fasahar zamani na HISBAH suna kan kokarin dawo da shafin hannun hukumar.
Saidai har yanzu shiru kake ji.
Da Sahara Reporters suka tuntubi hukumar ta HISBAH tace har yanzu tana kan kokarin kwato shafin daga hannun bata garin da suke da iko dashi.