Friday, December 5
Shadow

Har yanzu ina nan tare da shugaba Tinubu da jam’iyyar APC ban koma ADC>>Inji Sanata Abdulaziz Musa ‘Yar’adua

Sanata Abdulaziz Musa ‘Yar’adua ya bayyana cewa, ba gaskiya bane rade-radin da ake yadawa cewa wai ya bar jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar ADC.

Yace har yanzu yana nan a tare da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da gwamnan Katsina, Dikko Radda da kuma jam’iyyar APC.

Yace ba duka masu amfani da sunan ‘Yar’adua ne ke da alakar siyasa iri daya da tashi ba.

Ya zargi wasu kafafen yada labarai da neman yada jita-jita game da komawarsa ADC.

Yace amma shi Har yanzu dan APC ne kuma zai ci gaba da aikin da shuwagabanni dan kawo ci gaba da hadin kan Najeriya.

Karanta Wannan  Dalla-Dalla: Sanata Natasha Akpoti ta fitar da kalaman batsa da Sanata Godswill Akpabio ya gaya mata bayan da ta je ofishinsa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *